Manyan Hafsoshin Tsaro Za su Ci Gaba da Rike Mukamansu – Garba Shehu

0
115

Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa ya ce, manyan hafsoshin tsaron kasarnan za su ci gaba da rike mukamansu matukar shugaban kasa Buhari na gamsuwa da kokarinsu.

Garba Shehu, wanda ya fito a shirin gidan Talabijin na Arise jiya Litinin ya ce, kiraye-kirayen da ake yi na sauke manyan hafsoshin tsaro “Bai da tushe”.

Wasu sassan kasarnan dai na fuskantar hare-hare a yan watannin nan yayin da ake samun yawaitar sace mutane.

A karshen makon nan ne mayakan Boko Haram su ka halaka manoma sama da 40 a wani Kauye a jihar Barno.

Hakanne yasa wasu yan Najeriya ke ta kiraye-kirayen da a sallami manyan hafsoshin tsaron Najeriya.

Yayin tattaunawa da gidan Talabijin na Arise, Garba Shehu ya musanta batun cewa, lokacin manyan hafsoshin ya kare, inda ya ce doka ba ta iyakance lokacinsu ba.

“Ban san cewa wa’adin manyan hafsoshin tsaro yana cikin wata doka ba. Za su ci gaba da zama bisa ra’ayin shugaban kasa”, inji shi.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here