Ɓarayin Waya Sun Kashe Malamin Makarantar Al-Ƙur’ani a Kano

0
342

Wasu yan daba da ake zargin barayin waya ne sun dabawa wani malamin Al-Qur’ani wuka wanda ya kai ga rasa ransa a karamar hukumar Ungogo dake Kano.

Mutumin mai shekaru 34, mai suna Shu’aibu Bichi an kashe shi ne da tsakar ranar Juma’a a dakinsa.

Mazauna yankin sun shaidawa manema labarai cewa, yan daban sun lura cewa marigayi Shu’aibu bai rufe dakinsa ba yayin da suka yi amfani da wannnan damar wajen sace wayarsa.

Jabir Danrimi, mazaunin yankin ya ce ba wannan ne karon farko da al’ummar yankin ke fuskantar irin wannan lamari ba kamar yadda jaridar SAHELIAN TIME ta rawaito.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here