Yanzu-Yanzu: An Kama Abdulrasheed Maina a Kasar Nijar

0
288

Jami’an leken Asiri tare da hadin gwiwar jami’in hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya a yammacin yau Litinin sun cafke Abdulrasheed Maina a wani gari dake Kasar Nijar kamar yadda PRNigeria ta rawaito.

Wani babban jami’i a hukumar leken Asiri ya shaidawa PRNigeria cewa a samu nasarar kama Maina ne sakamakon kyakkyawar alaka dake tsakanin kasashen da kuma yarjejeniyar samar da tsaro.

Maina, tsohon shugaban kwamitin asusun yan fansho na kasa na fuskantar tuhume-tuhume har guda 12 tare da wani Kamfani.

Hukumar EFCC na zargi Abdulrasheed Maina da wawushe kudi har Naira Biliyan 2 wadanda daga ciki ya yi amfani da su wajen siyan kadarori a Abuja.

Haka kuma, ya ki halartar zaman kotu tun ranar 29 ga watan Satumba, lamari da ya kai ga Alkali n kotun, Justice Okon Abang ba da umarni tsare Sanata Ali Ndume wanda yake a matsayin wanda ya tsaya masa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here