Yadda Mayaƙan Boko Haram Su ka Yanka Ƴaƴana Biyu a Kan Idona – Wani Dattijo

0
268

Mallam Abubakar Yunus, daya daga cikin wadanda harin Zabarmari ya shafa inda ya rasa ya’yansa guda biyu, ya ce an kama su tare da ya’yansa kuma aka yanka su a gabansa.

“Mutane suna aiki a gonakinsu. A yankinmu, lamarin ya fara ne da karfe 10:30 na safe yayin da mayakan Boko Haram dauke da bindigogi suna sanye da kakin soji suka yi mana kawanya.

“Sun yanka ya’yana a kan idona kuma daya daga cikinsu ya tambaye ni su waye su a wajena! Na ce masa ya’ya na ne. Ina matukar kaduwa kan yadda mutane za su yi irin wannan rashin imani”, inji shi.

“Wadanda aka kashe su ne manyan gobe; matasa ne da aka kashe a lokacinsu da ake fi bukata; baza taba mantawa da wannan ba saboda an halaka al’umma guda. Sun tafi sun barmu mu dattijai da matansu da ya’yansu”, inji shi.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, manoma mata da yara sun noman shinkada a garin Zabarmari, kilk mita 25 da Maiduguri babban birnin jihar Barno.

Sannan rahotannin sun bayyana cewa mayakan Boko Haram din sun kone gonakin manoman.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here