Mata Masu Zaman Kansu a Sokoto Sun Fito da Tsarin “Ba Kwaroran Roba, Ba Jima’i” Don Kare Kansu daga cutar HIV

0
549

 

A yayin da Najeriya ke shirin gudanar da bikin ranar yaki da cuta mai karya garkuwar jiki, mata masu zaman kansu(Karuwai) a jihar Sokoto sun ce sun dauki matakin “babu kwaroron roba, babu jima’i” a wani bangaren na daukar matakin kare kansu daga kamuwa da cuta mai karyar garkuwar jiki.

Mata masu zaman kan nasu sun shaidawa kamfanin dillacin labarai na kasa(NAN) yau Litinin a Sokoto cewa sun dauki matakin ne don kare kansu daga cututtukan da ake yadawa yayin jima’i.

Sun ce cutar HIV gaskiya ce sannan kuma sun shawarci yan mata da manyan mata wadanda suke irin sana’arsu da su kare kansu daga cutar.

Daya daga cikin gidan karuwai da ke Sharp Corner a birnin Sokoto, wata budurwa mai zaman kanta a gidan ta fadawa kamfanin dillacin labarai na kasa NAN cewa ” tana yin duk mai yuwuwa don kare kanta daga cutar HIV”.

“Ina siyan Kwaroran roba da kudina saboda bana karbarsa daga wajen abokin harkata. Ina kokarin kare kaina kuma ina shawartar sauran yan mata da suke wannan sana’a su yi irin haka.

“Na aminta da cewa, ya kamata mu dinga amfani da kwaroran roba tare da duk wanda ya zo dakin mu. Yana da muhimmanci wajen kariya. Ina amfani da nawa.bana amfani da na abokin harkalla saboda duniyar nan ba gaskiya.

“Yanzu misali idan kai abokin harkata ne kuma kazo nan da kwaroran roba, ban zan yarda dashi ba. Duk irin kwarinsa ko kyansa. Zan yi amfani ne da nawa. Cutar HIV gaskiya ce dole ne ayi amfani da kwaroran roba.

“Ina zuwa asibiti duk bayan watanni uku don sanin yanayin lafiyata”, inji ta.

Wata yar shekara 22 wacce ta ke irin harkar wacce kuma ta ce ita ma’aikaciyar lafiya ce ta fadawa kamfanin dillacin labaran cewa ta na amfani da kwaroran roba don kare kanta daga cutar HIV.

“Nasan komai kan cutar HIV saboda na samu horo kan harkar lafiya amma na tsinci kaina a wannan harkar. Watakil bana ra’ayin aikin da nake yi amma ina son rayuwata.

“Don haka ba kwaroran roba ba saduwar jima’i” inji ta.

Ta ce: “Bazan taba kwanciya tare da kowa ba ba tare da kwaroran roba ba ko da zai bani kudade masu yawa. Wasu suna bani dubu 10 don mu kwanta da su ba tare da kwaroran roba ba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here