Majalisar Dokokin Jihar Kano ta Amincewa Ganduje Ya Ciyo Bashin Biliyan 20

0
112

Majalisar dokokin jihar Kano ta amince gwamnatin jihar ta ciyo bashin miliyan dubu 20 daga babban bankin Najeriya(CBN) da hadin gwiwa da bankin UBA don cike gurbin illar da annobar Korona ta yi wa tattalin arzikin jihar.

Yayin da yake karin haske kan wasikar da gwamnan ya aika majalisar wacce kuma shugaban majalisar ya karanta, shugaban masu rinjaye na majalisar, Hon. Kabiru Hassan Dashi ya ce zauren majalisar ya amince da bukatar ne bayan gwamnatin ta gaza samun bashin da ta nema a baya sakamakon tabarbarwar yanayin tattalin arziki.

Haka kuma Gwamna Ganduje ya nemi majalisar ta amince da sabuwar dokar kafa cibiyar koyar da sana’o’i ta Dangote Skill Acquisition.

Sannan gwamnan ya nemi amincewar majalisar wajen kafa dokar tafikar da kasuwannin Abubakar Rimi da Kasuwar Kantin Kwari don bunkasa harkokin kasuwanci a jihar.

A zaman majalisar na yau da kakakin majalisar, Rt. Hon. Abdul’aziz Garba Gafasa ya jagoranta, majalisar ta taya uwargidan gwamnan Kano, Hajiya Hafsat Abdullahi Umar Ganduje murna bisa bisa bikin cika shekara 63 da haihuwa.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here