Yadda Ƙungiyar Wakilan Kafafen Yaɗa Labarai ta Kano ta Karrama Fitattun Ƴan Najeriya

0
265

Kungiyar wakilan kafafen yada labarai ta Kano ta karrama mataimakin gwamnan jihar, Dr. Nasiru Yusif Gawuna, Dan majalisar wakilai, Rt. Hon Kabiru Alhassan Rurum, Barista Muhyi Magaji Rimin Gado shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano da sauran muhimman mutane bisa gudunmawarsu wajen ci gaban Kano da kasa baki daya.

Taron karramawar ya gudana ne a daren jiya Asabar a Bristol Palace Hotel Kano.

A yayin jawabinsa na maraba, shugaban kungiyar wakilan kafafen yada labarai ta Kano, Malam Ibrahim Garba Shu’aib ya ce kasancewar kafafen yada labarai a matsayin drika ta hudu dake tallafe da mulkin dimukuradiya, kungiyar wakilan kafafen yada labarai ta na matukar jin dadin alaka da gwamnatin jihar Kano musamman bisa sanya hannu kan dokar 003 da gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yi.

Mataimakin Gwamman jihar Kano tare da shugaban kungiyar wakilan kafafen yada labarai ta Kano da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Kano.

Yayin da yake jawabi daya daga cikin wadanda aka karrama din, tsohon shugaban majalisar dokoki ta jihar Kano, kuma dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Kibiya/Bunkure da Rano, Rt. Hon Kabiru Alhassan Rurum ya ce farin ciki ya mamayr shi yayin da ya samu kansa cikin wadanda kungiyar wakilan kafafen yada labarai za ta karrama.

Daga cikin wadanda aka karrama din sun hada da, ministan shari’a kuma antoni Janar na kasa, Abubakar Malami, shugaban hukumar fasahar sadarwa ta Kasa NITDA, malam Kashifu da kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Malam Muhammadu Garba.

Jami’in Hukumar Karota kenan yake karbar lambar karramawa daga dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Rano/Bunkure da Kibiya

Haka kuma, kungiyar ta karrama Malam Umar Haladu, wani dattijo dake aikin sa kai na gyaran hanya a titin Zoo road.

Sai kuma jami’in Karota, Malam Mansur Dawakin Kudi da Fauziyya D. Sulaiman wadanda aka karrama bisa kokarinsu wajen kyautatawa al’umma.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here