Wata Takwas da rufe Kasuwar Fatakwal: ‘Yan Kasuwa Sun yi Kira Ga Wike Ya Bude Musu Kasuwar

0
87

 

Daga Musa Muhammad Kutama,Kalaba

‘Yan kasuwa dake gudanar da harkokin kasuwancin su da na cinikayya a Babbar mayankar Fatakwal da ke unguwar masana’antu ta Trans Amadi sun yi Kira ga Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike, ya kaunaci Allah ya bude musu kasuwar da ya rufe tsawon wata Takwas ke nan.

Alhaji Ali Zariya ne ya Yi Kiran a zantawar sa da ‘Yan jarida a birnin Fatakwal,  ya ce “Ina Kira ga Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike da ya kaunaci Allah ya bude mana kasuwar mu da ke Babbar mayankar Fatakwal da ya kulle mana yace saboda cutar kurona”.

Kasuwar tun kafin bullar cutar kurona gwamnan ya rufe tsawon lokaci bayan bullowar cutar Tana nan a rufe har yanzu lamarin da ya jefa wasu daga cikin ‘yan kasuwar cikin mawuyacin Hali ta yadda wasu ma sun cinye jarinsu.

Alhaji Zariya yaci gaba da cewa “Kasuwar Babu irin kabilar Nijeriya da Babu cikin ta Tana gudanar da harkokin kasuwancin ta a ciki Amma ya kama ya rufe kasuwar saboda yarda da gurguwar shawara ta siyasa da wasu suka Bashi ” yana Mai zargi
Wannan al’amari ya Sanya matsalar rashin gudanar da sanao’in su a kasuwar ya kuntatawa rasuwar su .

Alhaji Ali Zariya ya kara da cewa “muna rokon Gwamna ya hadiye fushinsa ya bude mana kasuwa Inda muka samu muka makale muna sana’a ba kowa yasan wurin ba bare yazo gare mu”inji shi

Girman matsalar inji Dan kasuwar “ko lokacin da akayi yakin Basasar kasar Nan ba’a rufe kasuwanni ba Kuma mutane Basu Sha wahala haka ba kamar yanzu “inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here