Mutane 110 Boko Haram Ta Kashe a Jihar Barno – Majalisar Dinkin Duniya

0
145

 

Sashin Hausa na RFI ya wallafa labarin cewa, majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin mutanen da mayakan Boko Haram suka kashe a kauyen Kashobe da ke Jihar Bornon Najeriya ya kai akalla 110, sabanin 70 da Gwamnan Jihar Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayar bayan ya halarci jana’izar 43 da aka tattara gawarwakinsu yau da safe.

 

Shugaban Aikin Jin-kai na Majalisar Edward Kallon ya bayar da wannan sabon adadin wanda ya ritsa da fararen hular da ke aiki a gonar shinkafa.

Zulum da ya jagoranci jana’izar mutanen 43 ya ce, adadin na iya kai wa 70 saboda batar wasu mutane wadanda ba a iya gano inda suke ba.

Wannan shi ne karo na biyu da mayakan Boko Haram ke hallaka manoman a cikin wata guda, bayan 22 da suka kashe a watan jiya, lokacin da suke aiki a gona.

Kashe manoman ya dada harzuka ‘yan Najeriya wadanda ke kokawa kan tabarbarewar tsaro a yankin arewacin kasar da suka hada da ‘yan bindigan da ke kai hare-hare da kuma mayakan Boko Haram.

Ko a farkon makon nan, sai da Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya da kungiyar ACF ta ‘yan arewacin kasar suka koka kan tabarbarewar tsaro da kuma yadda zaman lafiya ya gagara a yankin arewacin kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here