Najeriya ta bukaci Ingila tayi bayani kan zargin Gowon

0
112

 

Sashin Hausa na RFI ya wallafa labarin cewa, gwamnatin Najeriya ta bukaci gwamnatin Birtaniya da ta nemi gafarar ta sakamakon zargin da wani dan majalisa Tom Tugendhat ya yiwa tsohon shugaban kasa Janar Yakubu Gown na sace rabin dukiyar kasar dake aje a Babban Bankin kasarnan lokacin da yake mulki.

Dan Majalisar ya shaidawa abokan aikin sa lokacin da ake zaman Majalisar cewar wasu mutane sun tuna lokacin da Janar Gowon ya bar Najeriya da rabin dukiyar kasar dake aje a Babban Bankin zuwa birnin London.

Tugendhat wanda shine shugaban kwamitin harkokin waje na Majalisar wakilai bai iya gabatar da wata shaida dake tabbatar da wannan zargi ba, amma kuma zargin na sa ya haifar da mahawara mai zafi a ciki da wajen Najeriya.

Wannan ya sa ma’aikatar harkokin wajen Najeriya tayi watsi da zargin inda ta kuma bukaci Gwamnatin Birtaniya da tayi Karin haske kan zargin ko kuma ta nemi gafarar Najeriya kan wannan zargi.

Charlotte Pierre, shugaban sashen dake kula da Afirka da kasashe renon Ingila a Majalisar yace matsayin Tugendhat ya sha banban Sarauniyar Ingila da kuma gwamnatin Birtaniya, saboda haka wannan matsayi ne na kan sa.

Pierre ya bukaci Gwamnatin Najeriya da jama’ar kasar da suyi watsi da kalaman Tugendhat.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here