Shin Kungiyar ASUU za ta Janye Yajin Aikin da ta Shafe Watanni 8 ta na yi a Gobe Juma’a?

0
133

Rahotanni sun bayyana cewa mafiya yawan shiyoyin kungiyar Malaman jami’o’i ta ASUU sun amince da tayin da gwamnatin tarayya ta yi kungiyar na tsame ya’yan kungiyar daga tsarin biyan albashi na IPPIS da biyawa kungiyar wasu bukatu don ta janye yajin aikin da ta ke yi.

Bayan tattaunawar gwamnatin tarayya da shugabannin kungiyar na kasa ne dai, ASUU ta fara tuntubar shiyoyinta don jin ra’ayinsu kan batun janye yajin aikin da kungiyar ta shafe tsawon watanni 8 ta na yi.

Shugaban kungiyar na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi a karshen makon da ya gabata yayin tattaunawa da manema labarai ya ce sai uwar kungiyar ta tuntubi rassanta kafin janyewa ko ci gaba da yajin aikin.

Kungiyar ASUU ta na yajin aiki tun watan Maris na wannan shekarar.

Kungiyar ta ce dukkan shiyoyin kungiyar wadanda suka kai 70 za su shiga yanke shawarar da za ta yi na janyewa ko akasin haka.

Ogunyemi ya ce ” Muna tuntubar mambobin mu. Yayin da muka samu sabon bayani zamu sanar.

“Zamu koma zama da gwamnati ranar juma’a. Shi ne lokacin da muka kammala tuntubar”.

Bayan amincewar da yawa daga rassan kungiyar ta ASUU abin jira a gani shi ne ko a gobe Juma’a kungiyar za ta janye yajin aikin da ta shafe watanni ta na yi?.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here