Manoman Najeriya Na Adawa da Shirin Bude Iyakoki

0
133

Yayin da Gwamnatin tarayya ke shirin bude iyakokin kasar da ta rufe na dogon lokaci sakamakon dakile shigo da kananan makamai da kuma haramtattun kayayyakin da ake shiga da su cikin kasarnan, wasu manoma sun bayyana rashin amincewar su da yunkurin gwamnatin.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wasu daga cikin manoman na cewar bude iyakokin zai baiwa kasashen makota shiga domin sayen abincin da ake da shi, matakin da zai haifar da hauhawan farashi.

Ministar kudi  Zainab Ahmed ta bayyana cewar nan bada dadewa ba gwamnati za ta bude iyakokin sakamakon gamsuwa da matakan da aka dauka na dakile shiga da haramtattun kayayyaki cikin kasar.

Ahmed tace kwamitin da shugaba Muhammadu Buhari ya kafa ya bada shawarar bude iyakokin, kuma yanzu haka yana nazarin rahotan da suka gabatar masa domin yanke hukunci a kai.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here