Ganduje Ya Amince da Naɗin Mahaifin Kwankwaso a Matsayin Mai Zaɓar Sarki a Masarautar Ƙaraye

0
279

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da nadin Musa Saleh Kwankwaso, mahaifi ga tsohon gwamnan jihar Kano, Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso, a matsayin daya daga cikin masu zabar Sarki a masarautar Karaye.

Tsohon gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso babban mai adawa da gwamna Ganduje tun da fari ya yi suka kan kirkirar sabbin masarautu a jihar da kuma cire tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi, wanda ya nada shi a shekarar 2014.

A wata sanarwa da ta fito daga jami’in yada labarai na masarautar Karaye, Haruna Gunduwawa, ya ce Musa Saleh wanda shi ne Makaman Karaye, za’a yi bikin nada shi a matsayin mai zabar Sarki tare da wasu mutum hudu.

Sauran masu zabar Sarkin sun hada da, Sarkin Bai, Jibrin Ibrahim Zarewa, Sarkin Dawaki Mai-Tuta, Bello Hayatu Gwarzo, Dan Iya, Bashir Mahe, da Madakin Karaye Ibrahim Ahmad, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Sannan wadanda a ka nada a matsayin yan majalisar Sarki su ne; Walin Karayr, Isma’ila Gwarzo, da Wazirin Karaye, Musa Muhammad wanda shi ne babban dan majalisar Sarki.

Ana tsammanin halartar gwamna, Wazirin Sokoto da wakilan masarautar Gwandu a bikin da za’a yi shi gobe Juma’a, 27 ga watan Nuwamba a masarautar Karaye.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here