
Sanata Elisha Abbo ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP tare da komawa jam’iyyar APC.
Sanatan mai wakiltar Adamawa ta Arewa a majalisar dattijai ya sanar da hakan ne a wasikar da ya rubutawa zauren majalisar.
Shugaban majalisar, Sanata Ahmad Lawan ne ya karanta wasikar a yau.
A wasikar, Sanata Abbo ya yi bayanin cewa ya yanke shawrar fita daga jam’iyyar PDP ne saboda yadda gwamnan jihar Adamawa Umaru Fintiri yake tafi da jam’iyyar ba dai-dai ba.