Nuna Goyan Baya Ga Abdul’aziz Yari a Matsayin Shugaban APC na Ƙasa Ya Haifar da Ruɗani

0
202

Nuna goyan baya ga tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari a matsayin wanda yafi da cewa da shugabancin jam’iyyar APC ya haifar da rudani a kungiyar yan takara a jam’iyyar.

A watan Yuni ne dai aka kafa kwamitin riko karkashin jagorancin gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni wanda zai tafiyar da jam’iyyar tare da tsara babban taron jam’iyyar cikin watanni 6.

Ko’odinetan kungiyar yan takara a jam’iyyar APC, Bashir Muhammed Yusif, a wata sanarwar da ya fitar a ranar Talata, ya ce Abdul’aziz Yari zai dawo da kimar jam’iyyar da kuma tabbatar da jam’iyyar ta ci gaba da rike madafun iko a shekarar 2023.

“Da zarar APC ta gaza samar da haziki jajirtaccen shugaba, yanayin da jam’iyyar ta samu kanta a zaben fidda gwani a shekarar 2019 zai iya kuma faruwa’ inji shi.

Kodayake, goyan bayan da kungiyar ta yi wa Abdul’aziz Yari ya samu tazgaro yayin da wata sanarwa da sakataren kungiyar na kasa, Sheriff Yusuf Banki ya fitar ya ce. An dakatar da Bashir Muhammed Yusif a matsayin shugaban kwamitin amintattun kungiyar a shekarar 2019.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here