Gwamnatin Tarayya ta ce Za’a Bude Iyakokin Najeriya da Su ke A Rufe Sama da Shekara Guda

0
238

Za’a bude iyakokin kasa(Boda) da aka rufe tun watan Agusta na shekarar 2019.

Ministar kudi, kasafi da tsare-tsare, Zainab Ahmed ce ta bayyana hakan yayin tattaunawa da wakilan kafafen yada labarai na fadar shugaban kasa a yau Laraba.

Zainab Ahmed ta ce kwamitin fadar shugaban kasa kan lamarin ya kammala aikinsa tare da bada shawarar bude iyakokin.

Ta ce kwanan nan kwamitin zai mika rahotansa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, bayan nan kuma za’a sanar da matsaya kan lamarin.

Kodayake ministan ba ta bayyana yaushe ne za’a mika rahotan ba da kuma har tsawon yaushe za’a sake bude iyakokin.

A watan Agusta na shekarar 2019 gwamnatin Najeriya ta rufe kan iyakokinta don dakile shigo da kwayoyi, kananun makamai, da kayan abinci daga kasashen yammacin Afrika.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here