Gwamnatin Kano Za ta Sauyawa Gidan Adana Namun Daji Matsuguni

0
302

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarnin sauya matsugunin gidan ajiye namun daji na jihar daga cikin birni.

Kwamishinan al’adu da yawon bude ido, Ibrahim Ahmed, ne ya bayyana hakan a yau Laraba, inda ya ce matsugunin gidan ajiye namun dajin na yanzu ba ya yiwa dabbobin dadi saboda basa son hayaniya.

Yayin da yake zantawa da gidan Rediyon Freedom, ya ce za’a mayar da gidan ajiye namun dajin zuwa garin Tiga dake karamar hukumar Bebeji a Jihar.

Ya ce “Muna aiki don sauya matsagunin gidan ajiye namun daji saboda matsagunin na yanzu mutane sun kewaye ahi. Yawancin dabbobin basa son hayaniya”.

“Za mu kuma sauyawa gidan matsuguni tare da gyrashi don mayar da shi irin na zamani”.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here