Gamayyar Ƙungiyoyin dake Yaki da Korona Za su Samar da Aikin yi Ga Matasan Najeriya Miliyan 4

0
213

Gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu dake yaki da annobar COVID-19(CACOVID), ta kaddamar da shirin samar da aikin yi ga matasa miliyan 4 da ware Biliyan 150 don bada tallafi a fadin kasarnan.

Shugaban gamayyar ta CACOVID kuma gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga manema labarai tare da shi akwai shugaban rukunin kamfanin Dangote, shugaban bankin UBA, Tony Elumelu da Manajan Bankin Access, Herbert Wigwe.

Mista Emefiele ya ce, da zarar an shawo kan matsalar rashin aikin yi za’a samu raguwar tashe-tashen hankula, inda ya bayyana cewa, rashin aikin yi tsakanin matasa na daga cikin abubuwan da suka taka rawa a zanga-zangar EndSARS.

Sakamakon haka ne, Mista Emefiele ya ce “CACOVID ta shirya kirkirar gagarumin shirin bunkasa ci gaban matasa wanda zai samar da ilimin fasaha da ilimin koyan sana’o’i ga matasan Najeriya miliyan 4 a shekaru biyar masu zuwa.

“Za’a horar da dalibai ayyukan hannu, gyran fanfo, aikin kafinta da sauran sana’o’in hannu.

” Ana tsammanin kashe Naira Miliyan dubu dari da hamsin wajen ganin aiwatar da shirin wanda za’a yi shi a cibiyoyin horarwa a fadin kasarnan”.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here