An yi Kira Ga Gwamnatin Kano Da ta Tallafawa Ma’aikaciyar Jinya ta Sa Kai da ta Rasa Kafafunta

0
293

Anyi Kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta tallafawa ma’aikaciyar jinya ta sa Kai a Ma’aikatar lafiya da kafafu biyu bayan da ta rasa kafafuwanta sakamakon hatsarin mota.

Shugaban Gidauniyar Tallafawa Mabukata Daga Tushe wato Grassroot Care & Aid Foundation Ambassador Auwalu Muhd Danlarabawa ne yayi wannan Kira bayan ganin halin da Khadija Umar ke ciki na neman agaji a kafafen sadarwa kuma har yanzu ba’a Dace da samun taimakon ba.

Auwal Danlarabawa ya Kara da cewa Anya Gwamnatin Jihar Kano Tasan da Matsalar da wannan baiwar Allah ke ciki kuwa a matsayinta na Mai taimakawa Ma’aikatar lafiya a asibiti ?

Muna Kira ga Gwamnatin Jihar Kano karkashin kwamishinan lafiya na Jihar akan a duba halin da wannan baiwar Allah Mai suna Khadija Umar wadda kafin tayi hatsarin mota tana bada gudunmawa a matsayin maaikaciyar jinya tasa Kai a asibitin Hotoron Arewa dake karamar hukumar Nassarawa. ( Voluntery ).

Khadija Umar dai ta samu hatsarin mota kuma sakamakon haka an yanke Mata kafafuwa biyu Inna lillahi wa Inna lillahi Raj’un rayuwar kenan kuma tana neman a taimaka Mata a Samar Mata da kafafu Kamar yadda akeyiwa wadanda aka yankewa kafa Dan samun sauki da rage radadi ma rashin kafafun masu.

Muna Kira da a duba irin gudunmawa da ta bayar a baya a Samar Mata da wannan kafa, hakan zaisa sauran Yan balantiri da suke ayyuka taimakawa Ma’aikatar lafiya jin kwarin gwiwar Cigaba da bada gudunmawa a kowanne lokaci, Wanda rashin hakan zaisa da yawa wasu su dauka baa damu da lafiyar su ba, ballantana a taimaka musu a lokacin da suke neman agaji duk da suka Yan asalin Jihar masu kishin Jihar da Al’ummar su.

Muna fatan za’a duba wannan Kira a taimakawa wannan baiwar Allah da take kwance a asibitin Aminu Kano AKTH A halin yanzu tana jiran tsammani, duba ga anyi Kira ga jamaa su taimaka Mata a kafafen sada zumunta kuma har yanzu shiru ba’a dace ba.

Amb Auwal Muhd Danlarabawa
Grassroot Care and Aid Foundation GCAF
( GIDAUNIYAR TALLAFAWA MABUKATA DAGA TUSHE) 08060257925 Kano Nigeria. 25/11/2020. ©

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here