
Hukumomin gidan gyaran hali na Kuje, Abuja a jiya Talata sun takaita samun damar ganin Sanata Ali Ndume, wanda kotu ta aika a gidan gyran halin bisa gazawa wajen gabatar da tsohon shugaban kwamitin fansho na fadar shugaban kasa, Abdulrasheed Maina, wanda yake a matsayin wanda ya tsayawa.
Mai shari’a Okon Abang na babbar kotun tarayya dake Abuja ya bada umarnin garkame Ndume bayan wanda ya tsayawa ya gaza bayyana a kotun tsawon lokaci.
Rahotanni sun bayyana cewa, wasu yan majalisa sun taru a gidan gyaran halin don ganin Ndume a ranar Talata.
An jiyo Sanata Elisha Abbo na PDP na fadawa Sanata Bala Ibn na’Allah cewa, jami’an gidan gyaran halin sun bukaci sahalewar babban konturolansu don bada dama a ga Sanata Ndume.
Sai dai wasu rahotanni sun bayyana cewa, sakamakon matakan kariya daga cutar Korona an dakatar da kai ziyara ga daurarru in dai ba lauyoyinsu ko matansu bane.