Ƴan Hisba sun Kama Wani Ɗan Sanda Bisa Zargin Yin Lalata Da Ƴan Mata a wani Gida a Kano

0
298

Yan Hisba sun kama wani jami’in dan sanda mai suna Basiru bisa zargin yin lalata da yan mata a Kano.

Basiru da wani mai suna Jamilu an yi zargin suna amfani da wani gida a yankin Rummawa dake karamar hukumar Ungogo a jihar Kano inda suke jan hankalin yan mata kanana da manyan mata wajen gamsar da su ta hanyar saduwa.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa asirin Basiru ya tonu ne yayin fa mazauna yankin suka sanarwa da yan Hisba bayan sun ga ya shigar da wata budurwa yar shekara 16 cikin gidan.

Wani Jami’in hukumar Hisba da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce “Al’ummar yankin sun yo korafi a kan gidan a lokaci da dama inda muka je muka kama wanda ake zargin tare da yarinyar”.

Tuni dai a ka tura lamarin zuwa ofishin yan sanda na Kwakwaci don yin bincike.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here