Ƙungiyar Wakilan Kafafen Yaɗa Labarai ta Kano Za ta Karrama Wasu Fitattun Ƴan Najeriya

0
200

Matamakin gwamnan jihar Kano, Dr. Nasiru Yusif Gawuna, Antoni Janar na kasa kuma ministan shari’a Abubakar Malami, Darakta Janar na hukumar sadarwa ta kasa(NITDA), Malam Kashifu Inuwa na daga cikin fitattun yan Najeriya da kungiyar wakilan kafafen yada labarai ta kungiyar yan Jaridu ta kasa reshen jihar Kano za ta karrama bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen ci gaba kasa da kuma karfafa gwiwar kafafen yada labaran Najeriya.

Haka kuma kungiyar za ta karrama: kwamishinan yan sanda na jihar Kano, Habu Sani da kwamishinan yada labarai na Kano, Malam Muhammad Garba, shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Barista Muhyi Magaji Rimingado, tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Kano, Kabiru Alhassan Rurum, da Alhaji Abubakar Mai fata shugaban kamafanin shinkafa na Umza.

A sanarwar da Sakataren kungiyar, Mustapha Hodi Adamu ya fitar ya yi nuni da cewar za’a yi taron karramarwar ne a ranar 28 ga watan Nuwamba, a Bristol Palace Hotel, dake Farm Center a Kano.

Sanarwar ta kara da cewa, wadanda za’a karrama din sun kasance mutane masu kima, wadanda suka yi aikin yabawa a fanninsu daban daban.

“Bayan lura da shugabancin kungiyar wakilan kafafen yada labarai da kwamitin tan-tancewa na karramawa, mun yanke shawarar karrama wadannan manyan mutanen bisa gudunmawarsu wajen ci gaban kasa, himmatuwarsu wajen samar da walwala ga al’umma a guraren ayyukansu da kuma kokarinsu wajen ci gaban kafafen yada labaran Najeriya”.

Sanarwar ta ce, an zabi wadanda za’a karrama ne bayan sun tsallake wasu matakan halaye da kwamitin ya duba.

Sanarwar ta kuma ce, duk wadanda za’a karrama din sun bayyana farin cikinsu na halartar taron.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here