Wata Kotu a Kano Ta Ba da Umarnin a Kama Shugaban Ƙaramar Hukumar Gaya

0
203

Wata kotu dake zamanta a Gezawa a Kano ta bada umarnin a kama shugaban karamar hukumar Gaya.

Mai magana da yawun kotunan jihar Kano, Babajibo Ibrahim ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano.

Ya ce lauyan wanda ke kara ya shigar da kara gaban kotun inda yake karar shugaban karamar hukumar Gaya da shugaban jami’iyyar APC na karamar hukumar.

Babajibo Ibrahim ya ce bayan karar da lauyan mai korafi ya shigar, babu daya daga cikin wadanda ake karar da ya gurfa gaban kotun wanda hakan yasa kotun ta bada umarnin kama su.

Rahotannin dai sun ce an zargi shugaban karamar hukumar ta Gaya da lakadawa Hafizu Mahmdu Gaya dantakarar shugabancin karamar hukumar duka yayin tantance yan takara.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here