Matsalar Tsaro Kullum Ƙara Taɓarɓarewa Take a Arewacin Najeriya

0
210

 

Ina mamakin yadda ake kashe al’umma a Arewacin Najeriya, A sace wasu domin ansar kudaden fansa, A kona mana dukiya a kuma saceta, A dauke Matan mu wasu abata musu rayuwarsu da sauran abubuwa marasa dadi da suke faruwa.

Yau gashi tun muna gani a wasu tsirarun jihohi abun yafara yaduwa zuwa sauran Jihohin Arewa, Tattalin Arzikin Arewa ya fara durkushewa, ankori manomanmu daga kauyukansu.

Ance idan gemun dan uwanka yakama da wuta kashafawa naka ruwa, Wlh idan bamu farka ba tun yanzu abunda muke gani anayi a sauran Jihohi wataran zamu wayi gari muga abun acikin Jihohinmu.

Muna da wakilai a fadar Shugaban Kasa, Muna da wakilai a majalissar tarayya da kuma ta dattijai, Manyan mutane da muke da su a Arewa, Matasan mu yan gwagwarmaya da muke dasu da kuma maluman addini.

Farawa da wakilanmu da muke dasu a fadar Shugaban Kasa, Majalissar Dattijai data Tarayya, Kuna ganin abunda yake faruwa a Arewacin Nigeria amma kunkasa yin wani abu takaimaimai wajen kawo qarshen wannan matsalar tsaron, Kowa yaja bakinsa yai shiru yakasa kare haqqin al’ummar dayake wakilta sai personal interest inku kukasan ku kare bayan kuna gani kullum ana kashe al’umma a yankinku basuji basu gani ba.

Wani abun takaicin wae Shugaban Committee na tsaro na Majalissar Tarayya dan Arewa ne amma banga wani kokari dayake akai ba domin kawo karshen wannan matsalar.

Sannan Maluman addininmu yakamata su farka wajen fadakar da gwamnati abunda yake faruwa, nanda Rahama Sadau tasa wani hoto dabai kamata ba Maluman addini har huduba suka dinga yi amma abun takaicin yau ana kashe rayukan al’ummar mu sunyi shiru yakamata su farka domin jan hankalin gwamnati wajen kawo qarshen matsalar nan.

Matasa muma yakamata mubada tamu gudunmawar dazamu iya wajen kawo qarshen matsalar tsaro a wannan yankin namu.

#EnoughOfNorthernKillings

Amb. Comr Abubakar Abdullahi Roba
abubakarabdullahiroba61@gmail.com
23 November, 2020.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here