
An yi garkuwa da wani babban Lakcara tare da matarsa a Jami’ar Ahmadu Bello Dake Zaria a jihar Kaduna.
Lackaran wanda ake kira da Bako, ya na sashin ilimin Physiology.
Wata majiya ta bayyana cewa, maharan sun kutsa gidan Lakcaran da safiyar yau Litinin.
A wata sanarwa da mai magana da yawun jami’ar, Auwwalu Umaru ya fitar ta tabbatar da faruwar lamarin.