Hari Kan Ayarin Gwamnan Jihar Borno Ya Laƙume Rayuka 8

0
312

 

Sashin Hausa na RFI ya wallafa labarin cewa, majiyoyin tsaro a Najeriya sun ce adadin wadanda suka mutu sakamakon harin kwanton bauna da ‘yan ta’adda suka kai wa wani ayarin motocin sojin kasar, dake bada tsaro ga gwamnan jihar Borno ya kai 8, biyo bayan gano wasu karin gawarwaki biyu.

 

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito cewa mutane shida da suka kunshi soji 5 ne suka mutu a harin, adadin da wata majiya ta dabam ta tabbatar.

Mayakan kungiyar IS shiyyar yammacin Afrika, dauke da maanyan bindigogi da na’urorin harba rokoki ne suka bude wuta a kan ayarin motocin soji da mayakan sa kai a kauyen Kwayamti, mai nisan kilomita 60 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.

Ayarin na kan hanyarsa ta zuwa garin Baga ne don samar da tsaro ga gwamna jihar Borno Baba Gana Umara Zulum wanda ya isa garin a jirgin sama mai saukar ungulu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here