Gidauniyar Tallafawa Mabukata Daga Tushe Ta Gudanar Da Taron Addu’a Kan Matsalar Tsaro

0
227

Gidauniyar Tallafawa Mabukata Daga Tushe Wato Grassroot Care and Aid Foundation GCAF ta gudanar da addu’a ta musanman kan Halin da ake ciki na ƙuncin rayuwa da kuma rashin kwanciyar hankali.

Gidauniyar ta gudanar da wannan taron addu’a ne karkashin jagorancin shugabanta Wato Ambasada Amb Auwal Muhd Danlarabawa tare da ɗaruruwan Yara Marayu da ake ɗaukar nauyin karatun su kuma suke zaune ƙarƙashin kulawar gidauniyar anan jihar Kano.

Ambasada Auwal Danlarabawa yayin gudanar da taron yace sunyi wannan addu’a ne na kwana uku Dan Neman Allah ya kawo ƙarshen yanayin da arewacin ƙasar ke ciki na tashin hankali da rashin tsaro tare da fargaba iri-iri da kuma ƙunci tare da talauci da tsadar kayan bukatu na yau da kullum da alumma ke ciki.

Danlarabawa yayi Kira ga Gwamnatin Tarayya da jihohin arewa da su tashi tsaye su kare rayukan al’umma da gina makoma Mai kyau wadda zata Samar da canjin yanayi Mai kyau, sannan yayi Kira ga malamai da limamai da Makarantu na islamiyya da kuma gidaje da a dukufa da yin addu’oi ba dare ba rana kan wannan Hali da aka tsinci Kai a ciki.

A ƙarshe Alh Auwal Danlarabawa yace zasu ci gaba da yin wannan addu’a a kowacce Rana da waɗannan yara Marayu kamar yadda suka Saba tare da yiwa ɗaukacin al’ummar da suke bawa gidauniyar Tallafi na ganin an inganta rayuwar wadannan yara Marayu da gidauniyar ke rike dasu sama da dubu Daya da ɗari biyar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here