Yanzu-Yanzu: Najeriya ta sake faɗawa cikin halin karayar tattalin Arziƙi

0
205

 

Sashin Hausa na BBC ya wallafa labarin cewa a hukumance, Najeriya ta sake faɗawa cikin halin karayar tattalin arziƙi, a cewar alƙaluman da Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya ta fitar ranar Asabar.

Tattalin arziƙin ƙasarnan ya ragu da kashi 3.62 cikin 100 a tsakanin watan Yuli zuwa Satumban 2020, a cewar National Beareu of Statistics (NBS).

Ƙasa na shiga karayar tattalin arziƙi idan adadin arziƙin da take samarwa a ƙasar ya ragu cikin wata shida a jere ba tare da ya farfaɗo ba.

A daidai lokacin da Najeriya ke ƙara shiga halin karayar tattalin arziƙi, hakan na nufin cewa darajar kuɗin Najeriya ta ƙara raguwa idan aka kwatanta da na sauran ƙasashe da ke gogayya da naira a kasuwannin duniya.

A shekarar 2016 ma sai da kasarnan ta fada irin wannan yanayi na karayar tattalin arziki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here