Kwamishinan Ƴan sandan Jihar Kano, CP Habu Sani Ya Raba Kayan Tallafi Ga Marayu a Kano

0
384

Kwamishinan yan sanda na jihar Kano, CP Habu Sani, a yau Asabar ya raba kayan tallafi ga marayu a jihar Kano.

CP Habu Sani ya ce rabon kayan tallafin na daga cikin bikin murnar cikarsa shekara 1 a ofis a matsayin kwamishinan yan sanda.

Jaridar PRIME TIMES NEWS ta rawaito cewa kwamishinan yan sandan ya dauki nauyin marayu da dama wajen koyan sana’o’i.

Yayin da yake jawabi a wajen bikin, Habu Sani ya bayyana ci gaba da nuna himmarsa wajen tabbatar da zaman lafiya a Kano, inda ya bayyana cewa Kano ce jiha mafi zaman lafiya a Najeriya.

Sama da marayu 200 ne suka amfana da tallafin a unguwar Hotoro.

A wani lamarin na daban kuma, CP Habu Sani ya gudanar da taron manema labarai a shelkwatar yan sanda dake Kano a yau Asabar.

Kwamishinan yan sandan ya bayyana manyan nasarorin da ya samu a shekarar, da suka hada da kawo karshen ayyukan masu aikata laifuka a jihar.

Ya ce rundunar yan sanda ta samu nasarar cafke daruruwan masu aikata laifuka wadanda suke aikata laifukan fashi, da masu kwacen waya.

“Mun kama sama da mutane 150 dake garkuwa da mutane tare da ceto mutane da dama”, inji shi.

Da yake magana kan zanga-zangar EndSARS da aka yi kwanan nan, Habu Sani ya bayyana farin cikinsa kan yadda rundunar yan sanda suka magance lamarin.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here