Kungiyar Malaman Jami’o’i ta ASUU ta yi Bayani Kan Batun Janye Yajin Aiki

0
234

Kungiyar Malaman jami’o’i ta ASUU ta fara tuntubar mambobinta domin yanke shawarar janyewa ko ci gaba da yajin aikin da ta ke yi.

Shugaban kungiyar na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi ne ya tabbatar da hakan yayin tattaunawa da jaridar THE NATION a yau Asabar.

Kungiyar ASUU ta na yajin aiki tun watan Maris na wannan shekarar.

Kungiyar ta ce dukkan shiyoyin kungiyar wadanda suka kai 70 za su shiga yanke shawarar da za ta yi na janyewa ko akasin haka.

Ogunyemi ya ce ” Muna tuntubar mambobin mu. Yayin da muka samu sabon bayani zamu sanar.

“Zamu koma zama da gwamnati ranar juma’a. Shi ne lokacin da muka kammala tuntubar”.

Yayin da aka tambaye shi ko kungiyar za ta janye yajin aikin kafin ranar Juma’a, sai Ogunyemi ya ce:

“Bani da karfin janye yajin aikin nan”.

A ranar Juma’a ne dai gwamnatin tarayya ta amince ta janye tsarin IPPIS ga mambobin kungiyar ASUU.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here