Har Yanzu Ƴan Bindiga Na Kai Hari Kan Ƙananan Hukumomi 3 na Jihar Katsina – Masari

0
238

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ce har yanzu yan bindiga da sauran masu aikata laifuka su na kashewa, fyade da yin garkuwa da mutane gami da sace dabbobi a kananan hukumomi guda 3 na jihar.

Masari yayin da yake zantawa da manema labarai a jiya ya ce, kananan hukumomin da abun ya shafa sun hada da Faskari, Sabuwa da Dandume.

Ya ce sauran manyan kananan hukumomi wadanda suka yi iyaka da dajin Rugu da jihar Zamfara, sun samu raguwar matsalar tsaro.

Ya ce rundunar sojan saman Najeriya ta kafa sansani a karamar hukumar Funtua saboda ayyukan yan bindiga, inda yace hakan zai bada damar saurin daukar mataki kan yan bindigar a yankin.

Masari ya ce sansanin rundunar sojan saman zai taimaka wajen kai hari ta sama kan inda yan bindiga ke gudanar da ayyukansu.

Ya ce “Guraren da kadai muke samun matsala su ne, Faskari, Sabuwa da Dandume, amma a sauran kananan hukumomi akwai zaman lafiya musamman Jibia, Batsari, Safana da Danmusa.

“Daga Rahotan da nake karna kowacce safiya, idan ka ga an samu matsalar sace shanu ko garkuwa da mutane, ya na faruwa ne a Faskari, Sabuwa da Dandume. Mun yi korafi ga hukumomin soji da su dauki mataki kan yankin Gurbi-Gidan Jaja-Kaura Namoda dake jihar Zamfara.

” Baza mu iya tseratar da Katsina ba har sai an samu tsaro a jihar Zamfara saboda kashi 99 na hare-hare da sace mutane dake faruwa a Katsina, daga Zamfara ne”.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here