Ƴan Sanda Sun Kama Matar Da ke Dafa Abincin Siyarwa da Ruwan Wankan Gawa

0
482

Daga Musa Muhammad Kutama, Kalaba

Ƴan sanda a jihar Akwa Ibom sun cafke wata mata da ake zarginta da yin amfani da ruwan da aka wanke Gawarwaki Tana dafa abincin sayarwa dashi.

Matar maisuna Gloria Edet na sana’ar sayar da abinci ne a Layin Itam dake Garin Uyo.

Asirin Edet ya tonu ne bayan da Wanda ta ke zuwa wurinsa Tana sayen ruwan da yayiwa gawarwakin wanka a dakunan da ake ajiye Gawarwaki na kudi yace yana binta Bashi kudi da ta sayi ruwan tsawon wata uku Bata biyashi ba.

Yaci gaba da cewa inji majiyar labarin mu cewa a kullum Sai tazo wurinsa sayen ruwan sau biyu sau uku a Rana Tana sayen.

Bangaren ‘Yan sanda kuwa sunce a binciken da suka Yi mata ta tabbatar musu da cewa da gaske ne Tana sana’ar sayar da abinci Kuma da ruwan da aka yiwa Gawa wanka take amfani dashi domin Duk Wanda yaci abincin ta Babu inda zai kara tafiya yaci abinci Sai ya dawo wurinta kuma Tana samun kudi sosai.
An mayar da matar zuwa Babban ofishin yansanda dake Uyo ana ci gaba da yi mata tambayoyi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here