Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Bukatar Kungiyar ASUU

0
365

Gwamnatin tarayya a yau Juma’a ta amince cewa za’a cire mambobin kungiyar ASUU daga tsarin biyan albashi na IPPIS.

A sanarwar bayan taro da ministan Kwadago, Chris Ngige ya fitar ta ce, gwamnati ta amince da bukatar kungiyar ASUU na biyan albashin mambobin kungiyar na watan Fabarairu zuwa Yuni ta kan tsohon tsarin GIFIMS.

Sannan gwamnatin ta bada damar kara yawan biyan alawus din da kungiyar ta ke bi daga Naira Biliyan 30 zuwa Biliyan 35 da kuma kara  kudin gyararrakin jami’o’i daga Naira Biliyan 20 zuwa biliyan 25.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here