Fitilar Ƙwai Ta Ƙona Jariri Jim Ƙadan da Haihuwarsa a Garin Kalaba

0
214

Daga Musa Muhammad Kutama, Kalaba

Wani Jariri ya samu mummunar kuna a Hannayensa da Kafafunwan sa ranar da aka haifeshi.

Fitilar kwai da aka makareta da kanazir ce sanadi tayi Bindiga wutar ta fantsama kan shimfidar da aka kwantar dashi Jim kadan da haifeshi wannan lamari ya faru a Kalaba Babban birnin jihar Kuros Riba,gidan unguwar zoma ta gargajiya.

Uwargida Stella Aluko da abin ya faru Tana wurin ta Fadi yadda hakan ya faru yadda abin ya faru tace “uwar yaron tazo gidan unguwar zoma ta haihu bayan haihuwar yaron Bata da kudin da zata biya unguwar zoma a sallameta kafin washe gari shine hakan Kuma ta kasance”.inji ta

Taci gaba da cewa ” Fitilar kwai da aka makareta da kanazir ce tayi Bindiga kananzir din ya watsu wutar ta bishi jariri Kuma na kwance “.

Bayan konewar hannaye da kafafuwa wasu sauran sassan jikin yaron da wuta ta saba ya kone.

Yanzu haka yaron na kwance a asibitin Victoria medical center dake Layin Ndidem Usong dake Kalaba ana jinyarsa

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here