Tsohon Malami a Kwalejin Fasaha Ta Kaduna Ya Kashe Kansa Tare da Harbin Matarsa

0
232

Mista Austin Umerah, tsohon malami a kwalejin fasaha ta jihar Kaduna ya kashe kansa a gidansa dake titin Kigo a jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Umerah ya harbi matarsa, Dr. Maurin Umerah Lakcara a sashin nazarin yare ta kwalejin kafin ya kashe kansa.

Matar tasa yanzu haka ta na karbar magani a Asibitin sojoji na 44 Reference Kaduna.

Jaridar ta Daily Trust ta rawaito cewa, lamarin ya faru ne ranar Laraba da misalin karfe 10 na dare.

Mai magana da yawun rundunar yan sanda ta jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige ya tabbatar da faruwar lamarin.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here