Mutane Biyu Sun Rasa Ransu Sakamakon Fadawa Rijiya a Kano

0
180

Mutum biyu sun mutu bayan sun fada rijiya a maban-bantan gurare a Kano.

Lamarin ya faru ne a unguwar Kwagar Kanawa dake Karamar hukumar Gezawa da Sabuwar Unguwa dake karamar hukumar Rano a jihar Kano.

Hukumar kashe gobara ta jihar yayin da ta ke tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar yau Alhamis ta ce ofishin yan sanda na Gezawa ya kira hukumar a waya da misalin karfe 8 na safe.

“Jami’an da ke kan aiki da suka isa wajen sun tarar da Yarinya ce yar shekara 9 mai suna Aisha Musa ta fada rijiya. An samu ceto ta cikin mawuyacin hali kafin daga bisani ta rasa ranta” inji kakakin hukumar, Malam Sa’idu Muhammad.

Ya kara da cewa, an mika gawarta ga mai garin Kwagar Kanawa, Alhaji Abubakar Usman.

A wani al’amarin na daban kuma, Sa’idu Muhammad ya tabbatar da cewa wani mutum mai shekaru 65, mai suna Isah Amadu Kamilu shi ma ya fada rijiya inda ya rasa ransa a unguwar Sabuwar unguwa da ke karamar hukumar Rano.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here