Matsalar Garkuwa da Mutane: Kullum Sai an Sace Mutum Aƙalla biyu a Kalaba – Bincike

0
196

Daga Musa Kutama a Kalaba

•Sace mutane ana garkuwa dasu:

•An sace sama da mutum 7 cikin mako daya a Kalaba.

Matsalar sace mutane ana garkuwa dasu domin Neman kuɗin fansa ta addabi mazauna Kalaba Babban birnin jihar Kuros riba.

Jihar na fama da Kalubalen ‘yan Kungiyar Asiri da basa ga maciji da juna .

Birnin Kalaba Wanda akewa lakabi da aljannar mutane yanzu wannan kirari na Neman dusashewa al’amarin da ya jefa mazauna Garin Kalaba da wasu kananan hukumomi a jihar Basu runtsawa da Ido biyu.

Binciken da aka gudanar ya nuna kasa da mako daya an sace sama da mutum bakwai a wurare Daban-daban a Kalaba da Kuma Karamar hukumar Akampa.

Masu sace mutanen kan zo da manya-manyan bindigu suna harbe-harbe domin tsoratar da jama’a daga nan Wanda suka zo kamawa Suma kama Sai su ingiza keyar sa cikin motar su ,su tafi dashi .

Wasu lokutan sukan Kira iyalan Wanda suka kama su nemi a Basu maƙudan kuɗaɗe daga naira milyan daya zuwa sama da haka har Sai abinda suka yanka a Basu ko su ka bukata .

Kwanan Baya an sa ce matar wakilin jaridar The sun a Kuros riba Judex Okoro da wasu lokitoci dake aiki a asibitin koyarwa na jami’ar Kalaba UCTH. Su uku sai da aka biya kudin fansa aka sako su lamarinda iyalan wadanda aka sace ke boyewa manema labarai adadin kudin da suka biya.

Wannan matsala ta girma ta yadda Duk Wani Mai Hannu da shuni ko Ma’aikacin gwamnati ke rufe wayarsa ko Rika komawa gida da wuri domin kaucewa Zama Wanda zai fada kamarsu.

Ta bangaren jami’an tsaro kuwa koda yaushe sukan Kare kansu da cewa Ba’a sanar dasu na ko Basu da labari.

Ranakun Litinin zuwa Laraba an sace mutum biyar a wurare daban -da ban ciki har da Mijin wata ‘Yar jarida anan Kalaba Mai suna Bassey Okon Essien da matar Wani tsohon dan majalisar wakilai Mai suna Ani Oku Ita bayan Mijin Mai suna Eno Patrick Orok Baya gida a layin Edi-motop dake Kalaba.

Irene Ugbo kakakin rundunar’Yan sandan jihar kuros riba dangane da lamarin tace “mafi yawancin mutanen da ake sa cewa Ba’a sanar damu”.

Wakilin mu ya zanta da Alhaji sha’aban Abdullahi sakataren Al’ummar Hausawa-fulani da al’ummar musulmi mazauna jihar Kuros riba kan wannan matsala Sai yace “Ba Wani abu muke fama dashi na face matsalar tsaro Babbar matsalar itace shi Gwamna Wanda shine Babban jami’in tsaro yaki ya kula da al’amarin”inji shi.

Yaci gaba da cewa “Nima akwai abokina Wanda ranar Lahadi aka bishi har gida aka dauke shi har yanzu Basu Kira ba ba’a san halinda yake ciki ba matsalar tsaro a kuros riba ta shiga Wani yanayi Mai ban tsoro”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here