Kotu Ta Bada Umarnin Kama Ɗan Atiku Abubakar Bisa Bijirewa Umarninta

0
313

Wata kotu a Kubwa, dake Abuja a yau Alhamis ta yi umarnin da a gaggauta kama Abubakar Atiku dan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Alkalin kotun, Bashir Danmaisule ne ya bada umarnin biyo bayan gazawar Atiku na bin hukuncin da kotun ta yanke na cewa ya mika ya’yansu guda uku ga tsohuwar matarsa Maryam Sherif.

Maryam, a shekarar da ta gabata ne ta kai karar Abubakar, a kotun Gudu wacce daga bisani aka sauya kotun zuwa kotu Kubwa, inda take neman kotun ta bata damar rike ya’yanta guda uku.

A ranar 27 ga watan Oktoba ne dai kotun ta yanke hukunci kan lamarin, inda ta bada umarni ga Abubakar da ya mika ya’yan nasu guda 3 ga matar da ya saka kuma mahaifiyarsu.

Sai dai bayan kin bin umarnin kotun lauyan Maryam Sherifa, Nasir Sa’idu ya bukaci kotun ta kirawo wanda ake karar ya bayyana a kotun don yin bayanin dalilan da yasa yaki bin umarnin kotun.

Kodayake, wanda ake karar tare da lauyansa, Abdullahi Hassan basu halarci kotun ba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here