Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Tarayya Ta Sanya Ranar Sake Zaman Tattaunawa da Kungiyar ASUU

0
175

Gwamnatin tarayya ta ce za ta koma tattaunawa da kungiyar malaman jami’o’i ta ASUU ranar Juma’a.

Ministan kwadago, Chris Nigige ne ya bayyana hakan a daren yau Laraba.

Ana tsammanin tattaunawar za ta mai da hankali kan batutuwa da aka jingine a baya, da suka hada da tsarin biyan albashi na UTAS da kungiyar ta gabatar.

Idan za’a iya tunawa dai, Kungiyar ASUU ta ki amincewa da tsarin biyan Albashi na IPPIS da gwammatin tarayya ta samar, inda ta dage kan amfani da tsarin UTAS wanda hukumar kula da fasaha ta kasa ke gwadawa a yanzu haka.

Mai magana da yawun ma’iakatar kwadago ta kasa, Charles Akpan, ya bayyana cewa, tattaunawa da shugabbanin kungiyar ASUU zai gudana ne a dakin taro na Ma’aikatar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here