Kotu Ta Umarci Ƴan Sanda Su Biya Diyyar Miliyan 3 Bisa Tsare Wani Mutum Ba bisa Ƙa’ida ba a Kano

0
188

Wata babbar koton tarayya dake zamanta a gyadi-gyadi, Kano, ta umarci rundunar yan sandan Najeriya da ta biya Naira Miliyan 3 diyya bisa tsare wani mutum mai suna Dayyabu Auwalu ba bisa ka’ida ba.

Kotun a hukuncin da ta yanke ta soki yan sandan bisa tsare Auwal Dayyabu har tsawon kwanaki 4 ofishin yan sanda ba tare da kai shi kotu ba.

Lauyan Auwal Dayyabu, Barista Abba Hikima ya fadawa kotun cewa, a watan Yuli na shekarar 2020, yan sanda su ka kama Auwalu bisa zargin hana yan sanda kama mahaifinsa.

Barista Abba Hikima ya kara da cewa, yan sanda sun kama tare da tsare Auwalu tsawon kwanaki 4 a ofishinsu ba tare gabatar da kara a gaban kotu ba.

Ya shaidawa, kotun cewa abinda yan sanda suka yiwa mutumin ya saba da yancinsa da yake dashi.

Kotun ta bada umarnin biyan diyyar miliyan 3 ga mutumin sannan kotun ta yanke hukuncin cewa yan sanda su nemi afuwar mutumin.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here