‘An Aikata Fyade Fiye da Dari a Kowacce Jiha a Najeriya Lokacin Dokar Kulle’ – MDD

0
157

 

Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta ce an samu rahotannin fyaɗe fiye da 3,600 a Najeriya baki ɗaya yayin da ake cikin dokar kullen anobbar cutar korona.

Mataimakiyar Sakataren MDD Amina Mohammed ce ta bayyana hakan, tana mai nuna damuwarta game da yawaitar cin zarafi mai alaƙa da jinsi a Najeriya.

Jaridar Punch ta ruwaito ta tana magana ne yayin ƙaddamar da wani taron ƙara wa juna sani kan cin zararfin mata da ƙananan yara mai taken Violence Against Women and Girls Situation Room.

Ta ƙara da cewa MDD za ta ci gaba da aiki da Ma’aikatar Harkokin Mata ta Najeriya domin ƙara tattara bayanai game da cin zarafin mata.

An gudanar da taron ne ƙarƙashin jagorancin MDD da Ƙungiyar Tarayyar Turai da Ma’aikatar Harkokin Mata ta Najeriya.

“Buƙatar irin waɗannan shirye-shiryen na da matuƙar mahimnmanci musamman a lokacin dokar kulle, wadda ta shafi duniya baki ɗaya,” in ji Amina Mohammed.

Ta ƙara da cewa: “Ministar harkokin mata ta ce adadin laifukan fyaɗe ya ninka sau uku idan aka kwatanta da lokutan baya. A lokacin dokar kulle, kowace jiha ta bayar da rahoton fyaɗe fiye da 100, abin da ya sa aka samu sama da 3,600 a ƙasa baki ɗaya, ” kamar yadda sashin Hausa na BBC ya wallafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here