Za mu Ci gaba da Yajin Aiki Har Sai Gwamnati ta Biya mana Buƙatunmu – ASUU

0
193

Kungiyar malaman makarantun jami’o’i ta kasa ASUU shiyyar Owerri ta yi ikirarin ci gaba da yajin aikin da take yi har sai lokacin da gwammatin tarayya ta biya mata bukatunta.

ASUU ta kuma bayyana yajin aikin da ta ke yi a matsayin na karshe da kungiyar za ta yi.

Ko’odinetan kungiyar shiyyar Owerri, Uzo Onyibinama ne ya bayyana hakan a yau Talata a taren manema labarai da ya gudana a jami’ar Nnamdi Azikiwe, da ke garin Awka a jihar Anambra.

Shiyyar kungiyar ASUU ta Owerri ta hadar da Jami”ar fasaha ta tarayya dake Owerri, jami’arOdumegwu Ojokwu, ta jihar Anambra da Jami’ar koyan aikin gona ta Michael Okpara da ke Imo

“Mun gaji da yajin aiki, wannan ne yajin aiki na karshe. Shi yasa muka ki janye shi har sai an biya mana bukatun mu. Bama sa yin wannan yajin aiki. Wannan ne na karshe”, inji shi.

Ya kara da cewa, gwamnatin tarayya na yiwa al’umma karya a kan yajin aikin nan, inda ya yi bayanin cewa babban dalilin yajin aikin shi ne gazawar gwamnati na mutunta yarjejeniyar da su ka kulla ba wai a kan tsarin biyan albashi na IPPIS ba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here