Malaman Kano Sun Buƙaci Majalisar Dokokin Kano ta yi Dokar Haramta Amfani da Kayan Faransa

0
266

 

Gamayyar kungiyoyin malamai dana ci gaban Al’umma a jahar kano sun nemi Majalisar Dokokin jahar kano ta kafa wata doka da za ta haramta amfani da kayan kasar Faransa da ayyukanta a jahar kano domin nuna fushi akan kalaman batanci da shugaban kasar Emmanuel Macron ya yiwa fiyayyen halitta Annabi Muhammad ( S.A.W) a kwanakin baya.

Da yake mikawa shugaban majalisar dokokin jahar kano bukatun kungiyar a rubuce, shugaban kungiyar Sheirk Ibrahim Shehu Maihula ya ce wani zama da malamai da kungiyoyin ci gaban al’umma a jahar kano suka yi ya amince a yi kira ga gwamnatin kano ta daina duk wata hulda da kasar Faransa da daina amfani da kayansu da kuma daina nazarin harshen Faransanci domin nuna damuwa da bacin rai akan kalaman shugaban kasar ta Faransa.

A lokacin da yake karanta wasikar, kungiyar a wajen ziyayar, Sheirk Ibrahim Mu’azzam Maibushira ya ce daukar wannan mataki zai nunawa kasar ta Faransa cewa al’umar musulmin Kano za su iya kare martabar fiyyen halitta da musulunci ga duk masu yi masa batanci.

A nasa jawabin shugaban majalisar dokokin jahar Kano Rt. Hon. Abdul’azeez Garba Gafasa, Walin Gaya ya nuna gamsuwarsa bisa hanyar da kungiyar ta bi wajen Isar da wannan sako a muhallin da ya dace inda ya ce majalisar a shirye take ta dauki matakin doka akan wannan babban al’amari da ya taba zukatun al’umar musulmin duniya.

Ya yi fatan malaman za su rika ankarar da majalisa dukkanin dokokin da suka shafi addinin musulunci da cigaba da fadakar da jama’a kima da darajar fiyayyen halitta da sahabbansa da kuma tarbiyyar addinin musulunci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here