Wata Kungiya Ta Yabawa Gwamnatin Tarayya Kan Yadda Ta Bawa Ibrahim Magu Damar Kare Kansa

0
113

Shugaban kungiyar matasan Arewacin Najeriya ta (NYF), Injiniya Bello Gambo Bichi ya bayyana gamsuwa kan yadda aka bai wa dakataccen shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati EFFC, Ibrahim Magu damar kare kansa kan zarge-zargen da ake yi masa lokacin da yake rike da hukumar.

Bello Bichi ya ce “Gwamnatin tarayya ta tabbatar da kimarta da kuma himmatuwarta wajen yin adalci da gaskiya bisa bayar da damar ga tsohon shugaban EFFC ya kare kan sa biyo bayan zarge-zargen da aka yi masa”.

A wata sanarwa da aka rabawa manema labarai yau Litinin a Kano, kungiyar matasan ta Arewa ta bakin shugabanta ta ce “yanzu ya bayyana cewa bisa tsarin bayar da dama sauraren ta bakin kowa da adalaci, gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin bincoke kan zarge-zargen da akewa tsohon shugaban EFCC.

“Gaskiya ta bayyana ganin yadda adalaci da bada dama ya taka muhimmiyar rawa a lokacin da gwamnati ta gayyace shi don kare kansa da kuma bashi dama” inji sanarwar.

Injiya Bichi ya kuma ki aminta da sanarwar da cibiyar HEDA ta fitar inda ta yi zargin cewa kwamitin binciken ya shafe kwanaki ba tare da samar da wani zargi na gaskiya ga tsohon shugaban EFCC din ba.

Ya ce, Ba a tauyewa Magu hakkinsa ba ta hanyar bai wa lauyoyinsa damar gabatar da bayanan su.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here