Masu Yiwa Kasa Hidima, Mutum 2 Sun Kamu da Cutar Korona a Kano

0
105

Aisha Tata, babbar mai kula da masu yiwa kasa hidima ta jihar Kano, ta ce cikin masu yiwa kasa hidima 826 da aka tura jihar an samu mutum biyu dauke da cutar Korona.

Babbar jami’ar ta bayyana hakan ne a yau Litinin yayin da ta ke yiwa manema labarai jawabi bayan rantsar da yan rukunin B na masu yiwa kasa hidima.

Ta ce wadanda su ka kamu da cutar an musu gwaji ne jim kadan bayan saukar su a sansanin kuma an tura su inda ya dace da kula da kafiyarsu.

Ta ce sai da aka yi masu yiwa kasa hidima 826 gwaji kafin a basu dama shiga sannanin su.

“Kamar yadda kuke gani, mun samar da dukkan kayayyakin kariya tare kuma da tabbatar da cewa duk wani mai yiwa kasa hidima ya yi amfani da su.

“Mun kuma tabbatar da yin feshi don ganin sansanin ya zama mai tsafta”, inji ta.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here