Gwamnatin Jihar Kano Za ta Inganta Kafafen Yaɗa Labarai Mallakarta

0
190

 

Gwamnatin jahar Kano ta yi alwashin inganta ayyukan kafafan yada labarai mallakarta a kasafin shekara mai zuwa ta 2021.

Kwamishinan yada labarai da Al’adu Comrade Muhammadu Garba ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga manema labarai na majalisar dokokin jahar kano bayan ya Kare kasafin kudin ma’aikatar a gaban kwamitin majalisar mai kula da harkoki Yada Labarai.

Ya ce gwamnati za ta kara kula da ayyukan Gidan Radio kano da Gidan Talabijin na ARTV da kamfanin Jarida na Triumph da kuma takwaransa na dab’i domin ganin suna yin aiki yanda yakamata.

Comrade Mohd Garba ya bayyana cewa ma’aikatar za ta yi yaki da ‘yan jarida na jabu wadanda ke zubar da kima da darajar aikin.

Kwamishinan yada labaran ya kara da cewa ma’aikatar za kuma ta rubanya aikinta na wayar da kan jama’a akan muhimmacin zaman lafiya da dogaro da kai da kiwon lafiya da kuma kare aiyukan da gwamnati ke samarwa daga bata gari.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here