Ɓarayi ne Su ka Mamaye Gwamnatin Buhari – Sanata Ali Ndume

0
159

 

Sashin Hausa na BBC ya wallafa labarin cewa, Sanata Ali Ndume mai wakiltar Mazaɓar Borno ta Kudu ya ce “ɓarayi” na cin amanar Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya “saboda su ne mafiya yawa a gwamnatinsa”.

Da yake magana a cikin shirin Sunday Politics na kafar Channels TV, sanatan ya ce duk da cewa Buhari ya yi bakin ƙoƙarinsa, akwai mutanen da ke yi wa gwamnatinsa zagon ƙasa.

Da aka tamnbaye shi ko maki nawa zai bai wa gwamnatin jam’iyyarsu ta APC bayan shafe shekara biyar a kan mulki, sai ya ce: “Magana ta gaskiya ba na jin daɗin yadda gwamnatin nan ke tafiya.

“Babban abin baƙin ciki shi ne, akwai abubuwan da suke faruwa waɗanda bai zama dole sai sun faru ba. Sau uku muna ƙoƙarin ɗaura shugaban ƙasa [Buhari] a kan mulki ba mu yi nasara ba, amma muka yi nasara a karo na uku.

“Na san Buhari mutumin kirki ne da ke son cigaban talakawa. Sai dai ɓarayi ne suka mamaye gwamnatin, abin da ya sa suke cin amanar tsare-tsaren da yake so ya gudanar.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here