Wata Budurwa, Ƴar aiki Mai Shekaru 16 Ta Rataye Kanta a Kano

0
405

Wata budurwa mai shekaru 16, mai suna Bahijja Gombe dake a matsayin yar aiki a wani gida dake rukunin gidaje na Zoo road karamar hukumar Birnin Kano, ta hallaka kanta a yau Lahadi.

Rahotanni sun bayyana cewa, Bahijja, wacce yar asalin jihar Gombe ce, ta kashe kanta ta hanyar rataya ba tare da barin wani jawabi ba.

Wata majiya ta ce, Bahijja wacce ke alhakin share-share a gidan ba ta zuwa makarantar Islamiyya ko ta Boko.

Sannan rahotanni sun bayyana cewa, an ganta a rataye cikin daki a daren jiya Asabar da misalin karfe 10

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce an kai gawar Bahijja asibitin Murtala Muhammad.

Ya ce an fara binciken abinda ya sabbaba rasuwar Bahijja.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here