Rundunar Ƴan Sanda ta Kama Jami’an Anti Daba Bisa Zargin Kashe Matasa Biyu a Unguwar Sharaɗa

0
351

Rundunar yan sanda ta kasa reshen jihar Kano ta kama wasu Jami’an sashin Anti Daba na Yan sanda wadanda ake zargi da kashe da matasa yan baruwanka guda biyu.

Mai magana da yawun rundunar ta yan sanda, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da kama jami’an, wadanda ya ce sun je unguwar Sharada don kama wasu yan daba tare da wasu da ba yan sanda ba a babur mai kafa uku sai dai lamarin ya juye zjwa rikici wanda hakan ya kai ga kisan matasan biyu.

Ya ce “Gaskiyane wasu jami’an Aniti Daba, bisa rakiyar wasu fararan hula a cikin Adaidaita Sahu sun je kama wash yan daba sai dai rahotannin sun bayyana cewa an kashe mutum biyu”.

DSP Abdullahi Haruna ya ce kwamishinan yan sandan jihar Kano, Habu Sani ya bada umarnin kama jami’an kuma an fara bincike kan lamarin.

Wani shaidar gani da ido ya tabbatar da labarin inda ya ce ” jami’an na Anti Daba sun je unguwar don su kama masu laifi sai dai sun bige da harbe-harbe kan mai uwa da wabi wanda hakan ya jawo mutuwar matasan guda biyu.

Tuni dai aka yi jana’izar matasan guda biyu, Abubakar Isah da Ibrahim Sulaiman (Mainasara).

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here