Ladi Bala Ta Zama Shugabar Ƙungiyar Mata Ƴan Jaridu Ta Najeriya

0
171

Ladi Bala ta gidan Talabijin na Kasa, NTA a jiya Asabar ta doke yan takara uku inda ta zama shugabar kungiyar mata yan jarida ta kasa wato NAWOJ.

An gudanar da zaben ne a garin Minna, babban birnin jihar Niger, inda Ladi Bala ta samu kuri’u 439 sai Aishat Ibrahim mai biye mata da kuri’u 251, yayin da Chindaba Danjuma ta samu 85, Ruth Abubakar ta samu kuri’u 48.

Ladi Bala wacce ta ke cikin farin ciki ta bayyana godiyar ta ga Allah madaukakin sarki sannan ta yi kira ga dukkan mambobin kungiyar da su hada kansu.

Sauran wadanda aka zaba sun hada da mataimakiyar shugabar kungiyar, Lilian Ogbano, Sakatariyar kungiyar Helen Udofia, mataimakiyar Sakatare Yinka Bode-Are, Ma’aji Fatima Rasheed, mai binciken kudi, Dorothy Abellaga da Kuma sakatariyar Kudi Adeola Adekunle.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here